Magajin Garin Birnin Nagasaki Na Kasar Japan Ya Ki Gayyatar HKI Taron Tunawa Da Kisan Kiyashin Yakin Duniya Na Biyu

Magajin garin birnin Nagasaki na kasar Japan ya ki amincewa da bukatar kasashen yamma na ya gayyaci wakilin HKI zuwa bukukuwan tunawa da harin makaman

Magajin garin birnin Nagasaki na kasar Japan ya ki amincewa da bukatar kasashen yamma na ya gayyaci wakilin HKI zuwa bukukuwan tunawa da harin makaman nukliya wanda kasar Amurka ta jefawa kasar a ranar 9 ga watan Augustan shekara 1945 wato a karshen yakin duniya na II.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin Nagasaki Shizo Suzuki yana cewa ba zai taba amincewa wakilin HKI ya halarci taron 9 ga watan Augusta ba.

Kafin haka dai kasashen yamma wadanda suka hada da Amurka, Burtaniya Canada, Faransa, Jamus, Italiya da kuma tarayyar Turai EU duk sun takurawa magajin garin, sun kuma yi masa barazana idan har ya hana wakilin HKI halattan taron, amma Suzuki  ya dage kan ra’ayinsa.

Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa mai yuwa mutanen kasar Japan su gudanar da zanga zanga ta yin allawadai da HKI kan kissan kiyashin da take aikatawa a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments