Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “

Shugaban Madagaska Andry Rajoelina ya bayyana cewa gagarumar zanga-zangar da akeyi a kasar, na da nufin “yi masa juyin mulki,” ne. A wani jawabi da

Shugaban Madagaska Andry Rajoelina ya bayyana cewa gagarumar zanga-zangar da akeyi a kasar, na da nufin “yi masa juyin mulki,” ne.

A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Rajaolina, ya yi ikirarin cewa matasan da suka yi gangami a kan tituna, da tun farko suke yin Allah-wadai da katsewar wutar lantarki da ruwan sha, wasu ’yan siyasa ne ke amfani da su.

A jawabi na tsawon mintuna ashirin da aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook, wanda shi ne na farko tun soma fara zanga-zangar, Shugaban kasar ta Madagaska ya tabbatar da cewa matasan da ake wa lakabi da ‘’G Z’’, ‘yan adawa” ne ke amfani da su wajen neman kawar da shi daga mulki.

Rahotanni daga kasar sun ce ko a wannan Juma’ar an ci gaba da zanga-zanga a babban birnin kasar inda ‘yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga zangar.

An dai soma zanga zangar ne tun ranar 25 ga watan Satumba domin nuna fishi kan matsalar wutar lantarki da kuma ruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted