Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Halin Tsaka Mai Wuya Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Shiga

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kai ga wani mawuyacin hali domin neman tsira Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kai ga wani mawuyacin hali domin neman tsira

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Gungun ‘yan ta’adda da ke rike da madafun iko a birnin Tel Aviv, sun kai ga matsala wajen yanke shawarar kare ci gaban rayuwar yahudawan sahayoniyya da wanzuwar shugabancinsu a haramtacciyar kasar da suka mamaye.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, Kan’ani ya fayyace cewa: Bayan watanni 11 na yakin hauka kan Zirin Gaza da kuma kisan gillar da aka yi wa al’ummar Falastinu sama da 41,000, an samu sabani tsakanin shugabannin yahudawan sahayoniyya wanda cikin sauri ya bazu kamar wutar daji, a cikin wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba, jami’an yahudawan sahayoniyya daga na soji da na tsaro suna mika takardun yin murabus din su tare da gudanar da zanga-zanga da yajin aiki a cikin sahu.

Kan’ani ya kara da cewa: A halin yanzu dai gibin da ake kara samu a cikin al’umma da cibiyoyin yahudawan sahayoniyya yana kara yin yawa a kan idon al’ummun duniya baki daya, ta yadda wasu shugabanni da masana yahudawan sahayoniyya suke bayani karara dangane da hatsari da tsarin rugujewar abin da ake kira da “Isra’ila”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments