Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi Fard; Duniyar musulmi tana fuskantar jarabawa mai girma da ita ce kare al’ummar Falasdinu, da takawa masu girman kai na duniya birki,haka nan ‘yan Sahayoniya ‘yan daba.
Limamin na birnin Tehran ya jaddada muhimmacin fuskantar ‘yan sahayoniya ‘yan daba a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.
Limamin ya tabo zagayowar ranar kafa tsrin jamhuriyar musulunci na Iran da kaso 98% na al’ummar kasar su ka kada kuri’ar amincewa da shi a 1979, yana mai jaddada cewa an kafa tsarin jamhuriya a Iran ne bisa koyarwa ta musulunci.