Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Juma’a Ya Ce: Dole Ya Sanya Isra’ila Ta Amince Da Dakatar Da Bude Wuta A Lebanon

Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: ‘Yan sahayoniyya sun gaza wajen kalubalantar ‘yan gwagwarmaya Limamin da ya jagoranci sallar

Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: ‘Yan sahayoniyya sun gaza wajen kalubalantar ‘yan gwagwarmaya

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a na birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hujjatul-Islam, Sayyid Muhammad Hassan Abu Tarabi Fard ya bayyana cewa: Wadanda suka ba da gudumawa wajen kifar da gwamnatin Siriya da kuma shirya yadda a ruguza ababen more rayuwa a wannan kasa, su ne ke da alhakin wurga  al’ummar musulmi da sauran al’ummar Siriya cikin mummunan halin da suka shiga a kasar.

Hujjatul-Islam Abu Turabi ya kara da cewa: Al’amuran kasar Siriya sun koma daya daga cikin muhimman batutuwan da dandalin siyasa yake tattaunawa a kai a ‘yan kwanakin nan.

Hakazalika, Limamin juma’a na Tehran ya bayyana gazawar yahudawan sahayoniyya wajen tunkarar gwagwarmayar Musulunci da kuma kasa cimma wata manufa da suka sanya a gaba a Falastinu da Lebanon, lamarin da ya tilasta musu amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah.

Ya kara da cewa: Gwamnatin ‘yan mamaya ta so ta boye kashin da kwasa a hannu, don haka da taimakon Amurka da hadin gwiwar wasu kasashen yankin ta huce haushinta kan kasar Siriya ta hanyar rusa ababen more rayuwa a wannan kasa.

Hujjatul-Islam Abu Turabi Fard ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sun kaddamar da hare-hare wuce gona da iri sama da sau 500 kan ababen more rayuwa da muhimman cibiyoyin soji da na leken asiri a kasar Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments