Limamin Sallar Juma’a A Tehran Ya Jaddada Bukatar Zaben Sabon Shugaban Kasa Da Ya Dace  

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya ce: Idan har sabon shugaban kasar da zai zo yana son sauya dukkan gwamnoni da

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya ce: Idan har sabon shugaban kasar da zai zo yana son sauya dukkan gwamnoni da ministoci, to hakan zai zama hasara ga al’ummar Iran

A hudubar sallar juma’arsa a yau a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, limamin da ya jagoranci sallar Juma’a Hujjatul-Islam Kazim Saddiqi ya bayyana cewa: Al’ummar Iran na bukatar shugaba mai gwazo himmar aiki da zurfin ilimi. Kuma idan duk wani sabon shugaban kasa ya zo da ke son kawo canji a wannan tsari da ke gudana ta hanyar musaya dukkan gwamnoni da ministoci, to zai janyo hasara ce ga al’ummar Iran, don haka akwai bukatar jama’a su zabi wanda zai ci gaba da bin tafarkin Shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi da tsare-tsarensa masu inganci da nagarta ga mutane.

Kazim Siddiqi ya kara da cewa: Ranar 14 ga wannan wata na Khordod hijira shamsiyya da muke ciki ita ce ranar hawan wani babban mutum matsayi na shugabanci da jagoranci, wanda ya samu damar sauya tarihi da tasiri a gabashi da yammaci. Saboda jagoranci wani hali ne da ya ke da mabambantan siffofi na fifiko ta fuskar kebantattun siffofi da darajoji da sanin hanya, don haka matsayin jagorancin malami masanin fikihu shi ne mafi kusanci ga jagorancin shugabannin shiriya, duk da shi ba katangagge ne ga aikata kuskure ba, amma mai tsantseni ne a fagen gudanar da ayyukansa don haka a tsawon rayuwarsa baya aikata wani laifi a kan son ransa da zabinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments