Hukumar Kwallon Kafa ta Libya (LFF) ta ce za ta ɗaukaka ƙara yayin da take kokarin soke takunkumin da aka kakaba mata bayan da aka soke wasan da ’yan wasan kasar za su buga da Nijeriya a gasar neman shiga gasar cin kofin Afirka a 2025.
Tawagar Super Eagles dai ta ki buga wasan ne da aka shirya fafatawa a birnin Benghazi bayan an karkatar da jirginsu zuwa wani filin jiragen sama na daban daga wanda aka tsara za su sauka, aka kuma jibge su a nan ba tare da wani bayani ba har na tsawon kusan sa’o’i 16.
Bayan haka ne kwamitin ladabtarwa na hukumar CAF ya bai wa Nijeriya nasara da ci 3-0 sannan ta ci hukumar LFF tarar dala 50,000.
Mukaddashin shugaban LFF Abdunnaser Ahmed ya shaida cewa; Ba za a iya ba da makin wasa ta haka ba.
Ya kara da cewa, “Duk wanda ya ki buga wasa kafin a soke wasan ya kamata a dauke shi a matsayin wanda ya yi rashin nasara.”
Matakin da CAF ta dauka ya bar Libya a tsaka mai wuya a gasar, saboda tawagar wasan kasar na bukatar lashe duka wasanninta biyu da suka rage a rukunin D, kuma ta yi fatan abokan karawarta Benin da Rwanda sun gaza samun maki.
Wata sanarwa da hukumar CAF ta fitar ta ce “duk wasu kararrakin wasu buƙatun neman sauki an yi watsi da su”, amma Ahmed ya tabbatar da cewa LFF za ta daukaka karar har zuwa kotun sauraron ƙararrakin wasanni (CAS) idan hakan ya kama.