Kasar Lebanon ta ce ta mika koke ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda ta bukaci da a yi Allah-wadai da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi kan kasar Larabawar tare da yin kira ga kasashen duniya da su dorawa gwamnatin mamayar alhakin laifukan da ta aikata.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Labanon ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi cewa, koken ya bukaci yin Allah wadai da mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunanta da kuma keta hurumin kasar, da kuma ci gaba da kai hare-hare kan al’ummarta.
Koken a cewar ma’aikatar ya bukaci tilastawa Isra’ila aiwatar da kuduri mai lamba 1701 na dakatar da yakin da take yi nan take da kuma janye sojojin Isra’ilar daga yankin na Lebanon.
Tun daga karshen watan Satumba, Isra’ila ta fara kai hare-hare ta sama da ta kasa kan kasar Labanon, bayan shafe kusan shekara guda ana yin musaya ta kan iyaka da kungiyar Hizbullah ta Lebanon dake goyan bayan al’ummar Gaza dake fuskantar yakin kisan kiyashin Isra’ila.