Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Sahayoniya A Garin Bint-Jubail

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint Jubail ya fuskanci hare-hare ta hanar amfani da jirgin sama maras matuki, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya.

Tashar talabijin din ‘almanar’ ta Lebanon ta ambaci cewa, wani jirgin “sra’ila” maras matuki ta jefa bom a kan wata motar  haka rami da hakan ya yi sanadiyyar konewarta, wanda shi ma sabon keta yarjejeniya ne.

Mahukunta a yankin na “Bint-Jubail” sun fitar da bayanin yin tir da abinda ya faru da ya yi sanadiyyar shahadar Ali Ibrahim Shitu wanda ma’aikaci ne.

Bayanin ya ci gaba da cewa harin ha Haramtacciyar Kasar Isra’ila” yana nufin dakile duk wani kokari na yi wa mutanen yankin himida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments