Lebanon: An Rufe Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Makwancinsa Na Karshe A Birnin Beirut

Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na

Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na Beirut,bayan da aka dauki tsawon yau ana gudanar da jana’izarsa.

Dubun dubatar mutanen Lebanon da kuma wasu daga wajen kasar ne su ka halarci taron jana’izar Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin da  aka gudanar a cikin birnin Beirtu.

Tashar talabijin din al’mayadin ta bayyana cewa bisa kirdado adadin mutanen da su ka halarci jana’izar sun kai mutane miliyan daya da 400,000.

Mahalarta jana’izar sun cika filin wasa na birnin Beirut da kuma manyan tituna ta yadda babu masaka cinke, da hakan ya sa motar da take dauke da makararsa da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin ta rike tafiya a cikin nawa.

An fara gudanar da taron jana’izar ne dai da takaitattun jawabai daga wakilin jagoran juyin musulunci na Iran da kuma na babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim.

A tsawon lokacin da motar dake dauke da makarar Sayyid Shahid take tafiya an rika watsa jawaban Shahidin da ya yi a lokuta mabanbanta a tsawon rayuwarsa da suke da alaka da yin jinjina ga al’ummar Lebanon,musamman masu bai wa gwgawarmaya kariya da goyon baya.

Lokaci kadan da ya gabata ne dai aka shigar da makarar da take da Sayyid Hassan Nasarallah cikin makwancinsa na karshe, a daidai lokacin da ake karanta suratu Yasin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments