Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma

Paparoma Leo XIV ya halarci  taron Musulunci da Kiristanci da tattaunawa tsakanin addinai a dandalin Shahidai da ke Beirut. Bayan isowarsa, Paparoma ya samu tarba

Paparoma Leo XIV ya halarci  taron Musulunci da Kiristanci da tattaunawa tsakanin addinai a dandalin Shahidai da ke Beirut.

Bayan isowarsa, Paparoma ya samu tarba daga shugaban Mabiya addinin kirista na Lebanon Bechara Boutros al-Rahi, da shugaban Mabiya darikar Katolika na Syria Ignatius Joseph III Younan, da kuma Babban Mufti na Lebanon Sheikh Abdul Latif Derian, da Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Mabiya mazhabar Shi’a a Lebanon  Sheikh Ali al-Khatib.

A lokacin taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Shi’a a Lebanon ya yi maraba da Paparoma, yana mai cewa: “Muna farin ciki da zuwnku a Lebanon a madadin Majalisar da kuma daukacin mabiya mazhabar shi’a na Lebanon, Muna maraba da kuma godiya da ziyararku zuwa kasarmu a wannan mawuyacin lokaci da kasarmu ke ciki.”

Ya ƙara da cewa: “Muna fatan ziyararku za ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa wadda ke fama da raunukan da hare-haren Isra’ila ke ci gaba da haifarwa na zalunci.”

Ya ci gaba da cewa: “Ba ma son ɗaukar makamai, kuma muna sanya alkiblar Lebanon ta zama a hannu na gari, muna fatan duniya za ta taimaka wa ƙasarmu ta sami zaman lafiya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments