A yau talata da yamma ce aka yi jana’izar shahidan Bintijbail na kudancin kasar Lebanon, wanda HKI ta kaisu ga shahada a lokacinda ta cilla makamai masu linzami kan motar da take dauke da su a ranar Lahadin da ta gabata.
Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, shahidan mutane 5 biyar ne wadanda suka hada da kananan yara 3 da mahaifinsu da kuma sannan mahaifiyarsu ta ji Rauni mai tsanani, da kuma yar’uwassu wacce itama ta ji Rauni.
Almanar ta nakalto cewa shahadar da kuma kissan kiyashin bai karawa mutanen garin ba sai karfin giwa na riko da kasarsu da kuma gwagwarmayansu.
Ministan kiwon lafiya Rakan Nasiruddeen tare da rakiyar minister watsa labarai Paul mahaifiyar yaran da yar’uwansu shikikiya, wadanda suke jinya a asbitin Jami’ar Amerika da birnin Beirut.
Nasiruddeen ya bayyana cewa ma’aikatarsa zata kula da masu jinya har zuwa samun lafiya.
Tun bayan da HKI ta bukaci a tsaida yaki tsakaninta da kungiyar Hizbullah kimani shekara guda da ta gabata, HKI take kaiwa mutanen kasar Lebanon yaki, inda suke kashe fararen hula tana kuma rusa gidajensu a duk ranar All..da sunan ci gaba da yakar Hizbullah.