Search
Close this search box.

Lavrov : An Kashe Nasrallah Ne Da Nufin Tunzura Amurka Da Iran Shiga Yaki

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, mutane da dama sun yi imanin cewa kisan da Isra’ila ta yi wa shugaban kungiyar

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, mutane da dama sun yi imanin cewa kisan da Isra’ila ta yi wa shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah na da nufin tunzura Iran da Amurka “shiga yakin basasa a daukacin yankin”.

Kashe shugaban Hezbollah “ba kisan gilla ba ne na siyasa kawai. Abin kunya ne, kamar yadda “Lavrov ya fada wa wani taron manema labarai bayan ya yi jawabi ga Babban taron Majalisar Dinkin Duniya a ranar Asabar.

Tunda farko dama Rasha ta “yi kakkausar suka ga” kisan Nasrallah, wanda ta ce “wani sabon kisa na siyasa ne da Isra’ila ta aikata,”

Ma’aikatar harkokin wajen Rashar a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce  Isra’ila na da “cikakken alhakin” sakamakon “mummunan” abun da kisan Hassan Nasrallah zai iya haifar a yankin.

“Muna kira ga Isra’ila da ta dakatar da tashin hankali” don “kawo karshen zubar da jini.”inji ma’aikatar harkokin wajen kasar Rashar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments