Laftanar Kanar Shikarci: Sojojin Iran Suna Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana Fiye Da Kowane Lokaci

Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka

Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya.

 Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta taba amfani da Kalmar ‘dakatar da fada ba” a mastayin zabi.

 Haka nan kuma ya ce; ‘Yan sahayoniya ba wadanda za a amince da su ba ne, balle gaskatawa, ba a cikin Iran ba, balle kuma a kowane wuri a duniya.”

 Shikarci ya kuma yi ishara da cewa; sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwan fiye da kowane lokaci a baya, don haka duk wani sabon hari na wuce gona da iri  daga ‘yan sahayoniya zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted