Kwamandan Rundunar Sojin Ruwan IRGC Ya Ce: Suna Iya Rufe Mashigar Hormuz Amma Ba Za Yi Hakan Ba Yanzu

Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Za su iya rufe mashigar Hormuz, amma ba za

Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Za su iya rufe mashigar Hormuz, amma ba za yi hakan a yanzu ba

Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Reza Tangsiri ya yi bayani kan irin fitattun abubuwan da jirgin ruwan da Iran ta kera mai suna Shahid Bahman Baqiri, inda ya ce; Wannan jirgi shi ne nau’i daya tilo saboda babu wata kasa a yankin yammacin Asiya da ke da makamancinsa.

Birgediya Janar Tangsiri ya bayyana a cikin shirin ”Labarin juyin juya hali” a tashar Al-Alam cewa: Bayan sanarwar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar dangane da alhakin da ya rataya a wuyan al’ummar Iran na gina rundunar sojojin ruwa ta tafi-da-gidanka a matakin juyin juya halin Musulunci. Domin samun damar tabbatar da tsaro ga magudanan ruwa na kasa da kasa da magudanar jiragen ruwa na Jamhuriyar Musulunci da kuma samun damar yin musanyar kayayyaki da na duniya, haka nan ma jiragen ruwa na duniya ma suna iya amfani da wannan hanya, to lallai ne dakarun kare juyin juya halin Musulunci su kasance a cikin teku. Domin kasancewa a cikin teku suna buƙatar manyan jiragen ruwa waɗanda za su iya kasancewa a can har abada kuma suna da wuraren da suka dace don gudanar da wannan aikin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments