Zababbun mambobi goma na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da E10, sun yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta a Lebanon.
Wannan bayani ya zo ne a matsayin martani ga karuwar tashe-tashen hankula da damuwa kan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Isra’ila suka kai kan dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon (UNIFIL), wanda ya faru a ranakun 10 da 11 ga watan Oktoba, inda aka jikkata dakarun wanzar da zaman lafiya hudu.
Kasashen na E10 sun jaddada cewa duk wani hari da ake kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Lebanon ya zama babban cin zarafi ga kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1701, Wanda aka samar domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a kan iyakar Isra’ila da Lebanon bayan rikicin shekara ta 2006.
Sanarwar ta yi nuni da wani koma baya mai tada hankali sakamakon gagarumin karuwar ayyukan sojojin Isra’ila a yankin.
Tun daga watan Oktoban shekarar da ta gabata, tashe-tashen hankulan da ake ci gaba da gwabzawa sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 45,000, lamarin da ya haifar da fargaba game da matsalar jin kai da ke kunno kai a kasar Lebanon da kuma yankunan da ke makwabtaka da ita.