Kwamandan Sojin Iran Ya Jaddada Kare Kan Iyakokin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Kwamandan sojojin kasa na sojojin Iran ya jaddada wajabcin Karin daukan matakan kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya

Kwamandan sojojin kasa na sojojin Iran ya jaddada wajabcin Karin daukan matakan kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya jaddada wajibcin kare cikakken kan iyakokin kasar akida, al’adu, da yanki, yana mai cewa: Dole ne dukkanmu al\umma su zama masu kare wannan kasa da kuma samun kwarin gwiwa daga tafarkin shahidai.

A yayin wata ganawa da iyalan shahidan kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyawa ta kakaba wa Iran a birnin Sarpol-e Zahab na lardin Kermanshah a ranar Larabar da ta gabata, Birgediya Janar Heidari ya bayyana cewa: Sojojin kasar suna kan gaba wajen kare ‘yancin kai da yankinsu na kasar, kuma a kodayaushe suna nuna godiya da irin hakurin da iyalan shahidan suke yi.

Ya kara da cewa: Tutar tsaro da tsayin daka za ta ci gaba da tashi har zuwa bayyanar Imam Mahdi (Allah madaukakin sarki ya gaggauta bayyanar da shi), kuma a ko da yaushe za ta kasance tana daga hannun mujahidai masu sadaukarwa.

Babban kwamandan dakarun sojin kasar Iran ya bayyana cewa: Shahidai masu haskaka hanyar daukakan ne da ‘yancin al’ummar Iran, kuma sun sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da tsaro da kuma abin alfaharin al’ummar musulmi a yau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted