Kwamandan Rundunar Kudancin Amurka ya sanar da murabus kan  batun  ayyukan soji a yankin Caribbean

Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da

Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da watan Disamba, saboda takun-saka tsakaninsa da sakataren tsaron Pete Hegseth, kan rashin jituwar da aka samu game da batun ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean.

Rahoton ya bayyana cewa, a makwannin da suka gabata ne Janar Holsey ya bayyana damuwarsa kan sahihancin wadannan ayyuka, yayin da Hegseth ya nuna takaicinsa kan yadda ayyukan ke tafiyar hawainiya, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin bangarorin biyu.

A cewar rahoton, manyan jami’an biyu sun tayar da jijiyoyin wuya ne a  yayin wani taro a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon a makon da ya gabata, inda suka yi musayar miyau da kuma yi wa juna zafafan kalamai, lamarin da ya kai ga sanar da murabus din Holsey a hukumance.

Janar Holsey ya karbi mukaminsa ne a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata kuma ya jagoranci Rundunar sojin Amurka a yankin Kudancin kasar a daidai lokacin da ake samun karuwar ayyukan sojin Amurka a yankin Caribbean.

Jaridar New York Times ta bayyana cewa Janar Holsey zai bar mukaminsa a karshen shekara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments