Search
Close this search box.

Kungiyoyin Kare Hakkin Dan’adam Sun Bukaci Ganin An Daina Bai Wa HKI Makamai

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama su 250 sun fitar da sanarwa wacce a cikin su ka bukaci ganin kasashen duniya sun dakatar da aika wa HKI

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama su 250 sun fitar da sanarwa wacce a cikin su ka bukaci ganin kasashen duniya sun dakatar da aika wa HKI makamai.

A yau juma’a gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil’adaman su 250 su ka fitar da sanrwar ganin an dakatar da kai wa HKI makamai, suna masu kara cewa; Aikin da ya rataya a wuyan kwamitin tsaron na MDD shi ne tabbatar da zaman lafiya da sulhu a duniya,hakan kuwa za ta tabbata ta hanyar dakatar da aike wa Isra’ila makamai.

Kasashen da su ka fi shigewa gaba wajen aike wa da HKI makamai su ne Amurka, Jamus da Birtaniya.

Daga fara yakin Gaza a watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun hara 33, yayin da wadanda su ka jikkata su ka haura 70,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments