Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta  Kama Olmert Da Livni

Gamayyar Kungiyoyin kare hakkin bil adama har da palastinian center for human right sun aike da takaradar korafi ga bangaren shari’a na kasar Kanada inda

Gamayyar Kungiyoyin kare hakkin bil adama har da palastinian center for human right sun aike da takaradar korafi ga bangaren shari’a na kasar Kanada inda suka bukaci a kamam tsohon pira ministan Isara’ila Egud Olmaert da kuma tsohowar ministan harkokin wajen isra’ila tzipi Livnin idan suka kawo ziyara birnin Toranto.

Zargin yayi dadai da dokar yaki da kare hakkin bil adama da kuma laifukan yaki mai lamba 146 na yarjejeniyar janeva da ta tilasta gwamnati ta kama wadanda ake zargi da keta dokokin , Olmert da Livnin suna da zarge-zarge akan su, da tafka laifukan yaki da kuma cin zarafin dan adama a shekara ta 2008 zuwa 2009 a yankin Gaza.

Olmert da Livni suna fuskantar zargi iri daya ne a kasashen turai ,inda a kasar birtaniya aka bada izinin kama livni a shekara ta 2009, wani sabon koke ya bullo ne bayan da jamian yan sanda na kasar Kanada za su fara bincike kan laifukan yaki a yakin da isra’ila take yi a yankin Gaza

Daga cikin laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa sun hada da kai hari kan fararen hula,yin amfani da sinadarin phospphurus a yankunan dake da cunkuson jama’a rusa gudaje da masallatai da kuma wuraren shan magani, da kuma makarantar majalisar dinkin duniya .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted