Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adam Sun Nuna Damuwarsu Da Halin Wadanda HKI Ta Tsare

Daruruwan masu rajin kare hakkin bil’adama wadanda suka shiga hannun HKI bayan da jiragen ruwan  da suka kwace jiragen ruwan da suka kawo su suka

Daruruwan masu rajin kare hakkin bil’adama wadanda suka shiga hannun HKI bayan da jiragen ruwan  da suka kwace jiragen ruwan da suka kawo su suka kuma kamasu suka tsare.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an tsare wadanda suke son karya killacewar da HKI tayiwa Gaza, a cikin gidan yari mafi tsaro a cikin HKI. Sun kuma bayyana cewa za’a tsare su na lokaci mai tsawo.

Kasashen da dama sun bayyana rashin amincewarsu da tsarewar da HKI ta yi wa wadanda masu neman a kawo karshen kill ace gaza. Sun kuma bukaci a sake su da sauri.

Daga ciki akwai Cyril Ramaphosa  na kasar Afrika ta kudu wadanda ya bukaci a saki dukkan yan kasar wadanda HKI ta tsare daga ciki har dajikan madugun kwatar yencin bakaken fata Monda Mandela.

Kasar Kuwaita da Malasiya duk sun bayyana cewa akwai yan kasarsu da aka kama, kuma sun bukaci HKI ta sake su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted