Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin falasdinu sun yi gargadi game da makircin da isra’ila ke kullawa na kashe  Marwan

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin falasdinu sun yi gargadi game da makircin da isra’ila ke kullawa na kashe  Marwan bargusu daya daga cikin  shuwagabanin falasdinawa a inda take tsare da shi a gidan yari,  samakamon gana masa azaba da aka yi .

Babban darektan kungiyar pps Amad Najjar yayi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa tun kafin lokaci ya kure game da abin  da israila ke kokarin yi kan marwan barghusi da hakan ya sabama dokokin kasa da kasa.

Haka zalika yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta ziyarci inda ake tsare da barghusi domin ganin irin halin da yake ciki,  kuma su matsa lamba na ganin an sake shi domin tseratar da rayuwasa .

Marwan Barghusu dan shakaru 66 da haihuwa da ake ganinsa a matsayin magajin shugaban gwamnatin falasdinu Mahmud Abbas yana tsare a gidan yari tun shekara ta 2002 an yake masa hukumci daurin rai da rai  saboda zargin da ake masa da hannu wajen yunkurin intifada ta biyu da falasdinawa suka yi da aka fara shekara ta 2000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted