Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca.
Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya.
Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.