Kungiyoyin Gwgawarmayar Falasdinawa Suna Cigaba Kai Wa Sojojin HKI Hare-hare A Sassa Mabanbanta

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 373, kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinawa suna cigaba da kai hare-hare a kan sojojin mamaya ta hanyar amfani

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 373, kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinawa suna cigaba da kai hare-hare a kan sojojin mamaya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da sauran makaman da su ka dace.

A sansanin ‘yan gudun hijira da HKI ta killace shi ta fuskoki daban-daban, kungiyoyin gwagwarmaya sun rika kai wa tankokinta na yaki hari da makamai masu huda silke, kamar kuma yadda su ka harba makamai masu linzami zuwa sansanonin ‘yan hijira dake kusa da Gaza.

Dakarun Kassam na Hamas sun kai wa sojojin mamayar hare-hare da su ka hada da rusa tankar yaki samfurin Mirkava 4 da makamin Shuwaz a kusa da hanyar “Safdawi dake yammacin Jabaliya. Bugu da kari dakarun na Hamas sun kai wani harin da makamin “Yasin 105” akan wata tankar yakin ta Mirkava, a kusa da makabartar “Faluja.

 Ita kuwa rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta kai hari da makamai masu linzami akan garin Asqalan na ‘yan share wuri zauna. Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa,an harba makamai masu linzami daga Gaza zuwa matsugunan da suke kusa da shi.

Rundar Shahid Abu Ali Mustafa da reshen soja ne na kungiyar “ Popular Front” ta sanar da kai hari akan sansanin ‘yan hijira na “Kisofim”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments