Bangarorin gwagwarmayar Palasdinawa sun mika sakon taya murna ga kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon kan zaben Sheikh Naim Qassem a matsayin sabon Sakatare Janar na kungiyar, tare da bayyana hadin kai da kuma amincewa da tsayin daka da kungiyar Hizbullah ta yi a yayin da take tinkarar sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da yunkurin mamaye kasar Lebanon.
Kwamitin gwagwarmayar Palasdinawa ya yaba da zaben Sheikh Qassem, tare da jaddada cewa yana nuna irin karfi da azamar Hizbullah.
Sanarwar tasu ta ce: “Zaben da majalisar shura ta Hizbullah ta yi, ya nuna karara cewa kungiyar za ta iya jurewa da kuma ci gaba da bin tafarkin gwagwarmaya da yahudawan sahyuniya.”
Majalisar Shura ta Hizbullah ta sanar da cewa ta zabi Sheikh Naim Qassem a matsayin babban sakataren kungiyar, wanda ya gaji Sayyid Hassan Nasrallah. Wannan shawarar, wadda ta ke da tushe a tsarin tafiyar da kungiyar Hizbullah, ta bi ka’idojin da kungiyar ta kayyade wajen zabar babban sakataren kungiyar, a cewar sanarwar ta Hizbullah.
Kungiyar ta bayyana kudirinta na ci gaba da yin riko da jagoranci na Sheikh Qassem, inda ta bayyana zabensa a matsayin wani muhimmin aiki
Kungiyar Hizbullah ta jaddada sadaukarwarra wajen ci gaba da gwagwarmaya, kamar yadda Majalisar Shura ta kungiyar ta bayyana fatanta na samun nasarar Sheikh Qassem wajen jagorantar kungiyar.