Kungiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana yada karya dangane da asibitin Kamal Adwan don kare kanta daga laifukan da ta aikata
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da laifukan da gwamnatin mamayar Isra’ila take aikatawa kan cibiyoyin kiwon lafiya, tare da yin kira da a dauki matakin hukunta ta kan hare-haren da take kaddamarwa kan cibiyoyin kiwon lafiya musamman bayan kona asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Zirin Gaza.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a jiya Juma’a ta yi watsi da kakkausar murya dangane da zargin yi amfani da cibiyoyin lafiya a gwagwarmayar da ta yi da ‘yan mamaya tana mai jaddada cewa: Babu wani bangare na sojojin Izzuddeen Al-Qassam ko kuma wani bangaren soji da ke amfani da cibiyoyin lafiya musamman asibitin Kamal Adwan da ke Zirin Gaza.