Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yaba da matsayin ‘yan gwagwarmayar Lebanon da al’ummar kasar Lebanon da suka nuna, lamarin da ya kai ga dakatar da kai farmakin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar ta Lebanon.
A cikin wata wasika da ya aikewa babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Qassem, babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu, Ziad Al-Nakhalah, ya taya al’ummar Lebanon murna da jinjinawa tsayin dakarsu, tare da taya murnar ci gaba da tsayin dakarsu a kan tafarkin shahidai.
Al-Nakhalah ya ce: jinjina ta tabbata a gare ku daga Falastinu zuwa Lebanon da kuma gwarzayen Gaza da mutanenta da ‘yan gwagwarmaya da al’ummar yankin kudancin Lebanon da dukkan al’ummar Lebanon masu juriya.
A cikin sakonsa, Al-Nakhalah ya kara da cewa ga Sheikh Na’im Qassim, babban sakataren kungiyar Hizbullahi “Tsarki ya tabbata a gare ka yayin da kake rubuta wannan tsayin daka da wannan karfi, kana kuma ka ci gaba da daga tutar tsayin daka tare da daukaka da alfahari tutar tsayin daka duk da raunukan da aka samu, kuma duk da hare-haren makiya, karkashin jagorancin Amurka da kawayenta.”