Kungiyoyi Sun Sake Fitowa Zanga-zanga A Fadin Faransa

A birnin Paris, zanga-zangar ta hada kungiyoyin kwadago, da dalibai suka shirya.

Kungiyoyi a faransa sun sake fitowa a zanga zanga a ranar Asabar ta biyar a fadin kasar kan tsadar rayuwa da tarin matsaloli sakamakon gazawar gwamnati.

Kare yara da matasa, albashi, ilimi sun ne suka dabaibaye zanga-zanga ta yau Asabar, Wanda ya samo asali daga fushin daliban makarantar sakandare.

An tsara yin zanga-zanga tsakanin wurare 50 zuwa 60 a duk fadin kasar, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar Laurent Nuñez, a yayin da aka jibge kimanin jami’an tsaro 70,000.

A birnin Paris, zanga-zangar ta hada kungiyoyin kwadago, da dalibai suka shirya.

A wasu manyan biranen kamar Bordeaux, Toulouse, da Rennes, ma an gudanar da zanga-zanga daban-daban wacce ta hada matasa da kungiyoyin kwadago.

A Marseille ma an gudunar da zangza zangar, yayin da a Lyon, zanga-zangar ta mayar da hankali kan sauyin yanayi da batutuwan matasa.

A faransa, zanga zangar da ta faro daga fishin daliban makarantun sakadare da na jami’a ta bazu zuwa ga kungiyoyin kwadago.

Matsalolin ilimi da suka daibaibaye makarantu, da tsadar rayuwa da kuma hauhawan farashin makamashi su ne matsalolin da suke damun faransawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted