Al-Husaini: Amurka Ta Keta sararin Samaniyar Iraki Har Sau 171

Kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bayyana cewa, sun lissafa yawan keta sararin samaniyar da jiragem yakin Amurka suka yi a kasar Iraqi har

Kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bayyana cewa, sun lissafa yawan keta sararin samaniyar da jiragem yakin Amurka suka yi a kasar Iraqi har guda 171 daga ranar 30 ga watan Satumban da ya gabata zuwa 23 ga watan Octoba, wanda keta yarjeniyar da aka cimma da ita Amurka ne kafin da fice daga kasar.

Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban kungiyar masu gwagwarmaya ta kasar Iraki Jaafar Alhusaini yana fadar haka ya kuma kara da cewa wadanan keta sararin samaniyar kasar Iraki bayan keta yarjeniya ya kuma dorawa gwamnatin kasar Iraki nauyi na bayani ga al-ummar kasar Iraki kan abinda yake faruwa.

A wani bangare Al-Husaini ya bayya cewa, rufe mashigar kan iyakokin kasar Iran da kuma zirga zirgar jiragen sama tsakanin Iran da Iraki, yana jingine da ganin damar Amurka ne. me ya sa hakan. Saboda yake yaken da Amurka da HKI suka farwa kasar Iran yaki ne tsakanin gaskiya da karya.

Kafin haka dai shugaban gwamnatin kasar Iraki kuma babban kwamandan sojojin kasar Ali Azzaidi ya bada sanarwan kawo karshen kawancen yaki da Daesh a kasar Iraki a karshen watan Satumban da ya gabata. Kuma daga lokacin kasar Iraqi gaba daya tana karkashin ikon gwamnatin kasar ne. idan haka ne me ya sa ake samun wannan keta sararin samaiyar kasar tare da jiraten yaki da kuma na liken asiri har 171 kamar yanda aka ambata?. Gwamnatin kasar Iraki, yakamata ta yiwa mutanen kasar bayanin abinda yake faruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted