Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da kungiyoyin fafutuka sama da 70 ne suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na kwace iko da yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kaura zuwa kasashe makwabta.
Wasikar da aka aike wa Donald Trump ta bayyana matukar damuwar kungiyoyin da suka sanya hannu kan shirin korar Falasdinawa kusan miliyan biyu daga kasarsu ta asali.
Wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun yi kira ga gwamnatin Amurka mai ci da ta karfafa yunkurin diflomasiyya a baya da ya kai ga tsagaita bude wuta a Gaza, maimakon aiwatar da manufofin da za su kawo cikas ga yankin yammacin Asiya.
A cikin wasikar da suka fitar sun ce matakin na Amurka kan Gaza na iya haifar da martani mai karfi daga kasashen Larabawa da na musulmi, da jawo sojojin Amurka cikin sabbin yake-yake marasa iyaka, wanda hakan zai haifar da karin rikici a yankin.”
Wasikar ta bukaci Trump da ya yi aiki da abokan huldar yankin don sake gina Gaza ba tare da korar mazaunanta ba.