Kungiyar Tsaro Ta Nato Ta Zabi Ci Gaba Da Yaki Da Rasha Bayan Taronta Na Washington

A wani bayanin bayan taron wanda ta fitar bayan taron shuwagabanninta a birnin Washington na kasar Amurka, kungiyar tsaro ta NATO ta ce ta zabi

A wani bayanin bayan taron wanda ta fitar bayan taron shuwagabanninta a birnin Washington na kasar Amurka, kungiyar tsaro ta NATO ta ce ta zabi ci gaba da yakar Rasha a Ukraine maimakun duk wata hanyar tattaunawa don dawo da zaman lafiya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran AP na kasar Faransa ya nakalto kungiyar mai kasashe 32 tana fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa ta zabi ta ci gaba da goyon bayan da take bawa gwamnatin Ukraine, don takurawa kasar Rasha.

Labarin ya kara da cewa, kasar Ukraine ta kuma kama hanyar zama mamba a cikin kungiyar tsaro ta NATO, ba makawa.

Banda haka kasashen sun kara da cewa a cikin sabon shirin taimakawa kasar Ukraine, kasashen Amurka, Nertherlands da kuma Denmark zasu isar da jiragen yaki samfurin F-16 zuwa ga matukansu yan kasar Ukraine a karshen watan Decemba mai zuwa.

Amma Jeffrey Sachs wani masanin harkokin tattalin arziki kuma ma’aikacin MDD ya bayyana cewa zabin da shuwagabannin Nato suka yi a Washington ya nuna irin yadda Amurka take mamaye da kungiyar, kuma ba wata daga cikin kasashen kungiyar da suka isa su taka mata burki.

Jeffrey ya kara da cewa babu wata kasa daga cikin kasashen kungiyar tsaro ta NATO wacce take tunanin hanyar tattaunawa da kasar Rasha kuma sun yi watsi da juyin mulkin shekara ta 2014 da kuma yarjeniyar Minsk da ta rushe, da kuma shirin fadada kungiyar tsaro ta NATO wanda su ne matsalolin kasar Rasha na asali da Ukraine kafin a shiga yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments