Kungiyar tarayyar Turai Ta Bukaci A Warware Rikicin Gaza Cikin Lumana Ba ta Hanyar Yaki Ba

Mai kula da siyasar waje  ta kungiyar tarayyar Turai Jose Borell ya yi kira da a dauki duk wani mataki da zai hana afkuwa tashin

Mai kula da siyasar waje  ta kungiyar tarayyar Turai Jose Borell ya yi kira da a dauki duk wani mataki da zai hana afkuwa tashin hankali a yankin kuma a mayar da hankali wajen ganin an kawo karshen yakin Gaza cikin lumana .

Borell ya fadi haka ne a wajen taron ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai a kasar Italiya kuma ya kara da cewa yankin yammacin Asiya yana gab da fadawa cikin wani rikici , wanda sakamakonsa zai shafi duniya baki daga  ciki har da kasashen turai don haka wajibi ne a kawo karshen  yakin da Isra’ila ta kaddamar a yankin Gaza cikin gaggawa

Haka zalika da yake ishara game da martanin ladabtarwa na Alkawarin Gaskiya da Iran ta kai wa Isra’ila ya fadi cewa iran ta yi amfani da hakkinta da doka ta bata na kare kanta  kamar yadda yake a kudurin doka ta 51 ta majalisar dinkin duniya .

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments