Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu
Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.
A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar shirun da kasashen duniya suka yi dangane da halin da ake ciki a Gaza da kuma jaddada ci gaba da goyon bayan kungiyar Tarayyar Afirka ga Falasdinawa. Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki ya ce: Sun ga yadda duniya ta yi shiru duk da wannan mummunan yanayi da al’ummar Gaza ke ciki, har ma wasu daga cikinsu na yin kira da a kori Falasdinawa daga muhallinsu, lamarin zai kara ta’azzara mummunan kangin da Falasdinawa suka shiga.