Sakatare-Janar na Majalisar Hadin Kan Kasashen yankin tekun Farisa ya bayyana batun kafa Isra’ila babba a matsayin Baban hadari da ke barazana ga dukkanin kasashen larabawa.
A wata hira da jaridar Al-Qabas ta Kuwaiti, Jassim Mohammed Al-Budaiwi ya fada a wannan Lahadin cewa, kasashe mambobin kungiyar (GCC) sun yi watsi da duk wani buri na fadada Shirin da ake kira da Isra’ila Babba a cikin yankin kasashen Larabawa.
Kasashen mambobi sun yi gargadin illar da wadannan buri ke ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ya kara da cewa mambobin kawancen sun tsaya tsayin daka tare da al’ummar Palasdinu dangane da harin wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza, musamman yin Allah wadai da zaluncin da sojojin mamaya ke aikatawa kan fararen hula.
A wani bangare na jawabin nasa, Al-Budaiwi ya nanata yin Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan kasar Siriya, musamman kutsen da sojoji suka yi a yankin wanda ba a saba ganin irinsa ba, tare da keta hurumin kasar Siriya.
Ya kuma jaddada goyon bayan kawancen ga ‘yancin kai, tsaro, da ‘yancin kasar Lebanon.