Search
Close this search box.

Kungiyar Kasashen Musulmi Sun Bukaci Kasashen Duniya Su Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu Mai Cikekken Yenci

Kungiyar Kasashen Musulmi ta OIC wacce take taronta na 15 a kasar Gambiya a halin yanzu ta bukaci kasashen duniya wadanda har yanzun basu amince

Kungiyar Kasashen Musulmi ta OIC wacce take taronta na 15 a kasar Gambiya a halin yanzu ta bukaci kasashen duniya wadanda har yanzun basu amince da kasar Falasdinu mai zaman kanta ba, da su yi hakan da gaggawa.

Majiyar kamfanin dillancin labaran IRIB NEWS ta bayyana cewa kasashen sun bukaci kasashen duniya su amince da kasar Falasdinu mai zaman kanta a kan iyaka na shekara ta 1967 wacce take da babban birni a gabacin birnin Kudud. Banda haka falasdinawa wadanda suke gudun hijia a kasashen duniya daban daban suna da hakkin komawa kasarsu.

Kungiyar ta yi wannan bayanin ne bayan da kasashe Trinidad and Tobago wadanda suke kudancin Amurka a taken carabian suka shelanta amincewa da samuwar kasar Falasdinu mai cikekken yenci kamar ko wace kasa a duniya.

Batun yaki a gaza shi ne ya mamaye taron kasahsen musulmi 57 na kwanaki 2 a birnin Banjul na kasar Gambiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments