Yahudawa Sun Firgita Sakamakon Hare-Haren Hizbullah

Kungiyar Hizbullah ta tarbi sojojin mamayar Isra’ila ta hanyar halaka sojoji masu yawa daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama a ranar farko da

Kungiyar Hizbullah ta tarbi sojojin mamayar Isra’ila ta hanyar halaka sojoji masu yawa daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama a ranar farko da suka sanar da fara kai farmaki ta kasa a kasar Lebanon

A ranar farko da rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka sanar da fara kai farmaki kan yankin kudancin kasar Lebanon ta kasa, rundunar sojin ‘yan mamayar ta fara karbar mummunar Bushara ta hanyar samun tabbacin halakar sojojinta masu yawa tare da jikkatan wani adadi mai yawa, lamarin da ya kada hanjin ‘yan siyasar yahudawan sahayoniyya.

Rahotonni sun bayyana cewa: Ranar farko da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka fara kaddamar da farmaki ta kasa a kudancin Lebanon ta kasance abin kaduwa ga dukkan matakai na soji da siyasa da kuma kafofin yada labarai. Inda ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullahi suka yi kwanton bauna ga sojojin tare da samun nasarar halaka wasu daga cikinsu baya ga jikkata wasu da dama baya ga yinluguden bama-bamai kan sansanonin sojin yahudawan Sahayoniyya.

Majiyar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da halakar sojojin cikin har da manya jami’ai tare da jikkata wasu da dama bayan watsuwar sojojin haramtaciyar kasar Isra’ila a kan iyakar kasar Lebanon a ranar farko ta aniyasu ta kaddamar da hare-hare kan kudancinLebanon ta kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments