Mataimakin sakatare Janar din kungiyar hizbullah ta kasar Labanon shaikh Na’im Qasim ya bayyana cewa martanin Hizbullah zai kasance mafi muni inda gwamntin Isra’ila ta yi gigin kai mata hari, yace taimakawa Gaza da take yi ya kawo cikas sosai ga mummunan nufin Isra’ila a yankin falasdinu da ma kasar Labanon.
Har ila yau ya kara da cewa dole ne a kawo karshen yakin Gaza kafin a Dakar da kaihare-haren daga labanon, ya zama wajibi duniya ta farka ta kawo karshen kisan kiyashin Isra’ila a Gaza domin shi ne abin da yafi dacewa.
Sheikh Na’im ya kara da cewa hizbullah tana mayar da martani da ya dace ga makiya , gwargwadon yadda makiya suka fadada yakinsu gwargwadon yadda Hizbullah take mayar musu da martani, yazuwa yanzu ta harba makamimai linzami fiye da dubu 4 da kuma makami mai tarwatsa tanka guda dubu 6 ga israila daga lokacin fara yaki zuwa yanzu.