A wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa; A karkashin taimakawa Falasdinawa da kuma kare mutanen Lebanon, sun kai hari akan sansanin soja na “Doviv” ta hanyar harba makamai masu linzami.
Bugu da kari dakarun na Hizbullah sun sanar da harba makamai masu linzami fiye da 30 zuwa garuruwan Nahariya, Safad da kuma Haifa.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa an ji karar fashewar abubuwa masu yawa a cikin garin Haifa sanadiyyar makamai masu linzamin da aka harba daga Lebanon.
A fagen dagar yakin kasa kuwa, sojojin HKI da su ka fara kutsawa a kudancin Lebanon tun a ranar 23 ga watan Satumba, har yanzu ba su iya kama ko da kauye daya ba.
A jiya Litinin ma dai dakarun kungiyar ta Hizbullah sun sanar da kai wasu hare-haren akan masana’antar hada abubuwa masu fashewa a garin Khudhairah dake kudu da birnin Haifa. Kungiyar ta Hizbullah ta sanar da harba makamai masu linzami da dama akan wannan masana’anta.
Sojojin na mamaya sun yi kokarin kutsawa cikin garin Marun-Ra’as a jiya da dare, sai dai harin da dakarun na Hizbullah su ka kai musu da makamai masu linzami ya tilasata su janyewa.