Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Tana Ci Gaba Da Luguden Wuta Kan Yahudawan Sahayoniyya

Kungiyar Hizbullahi tana ci gaba da harba makamai masu tada                                                                                                                                                                          gobara a arewacin Isra’ila tare da jefa bama-bamai kan birnin Haifa Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta

Kungiyar Hizbullahi tana ci gaba da harba makamai masu tada                                                                                                                                                                          gobara a arewacin Isra’ila tare da jefa bama-bamai kan birnin Haifa

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon na ci gaba da kai hare-hare kan sojojin mamaya, sansanonin soji da kuma matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke arewacin Falastinu da aka mamaye, kuma a yau ta kai hari da wani nau’in makami mai linzami kan sansanin Tirat al-Karmel da ke kudancin birnin Haifa.

Mayakan gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon a jiyalahadi sun kai hari kan sansanin “Filon” da ke Rosh Pina a gabashin birnin Safed da aka mamaye, da wani katon makami mai linzami.

Sannan ‘yan gwagwarmaya sun kai hari kan wani taron sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila a Wadi Hunin da ke yammacin garin Adissa da makami mai linzami, inda suka janyo halakar sojoji masu yawa tare da jikkata wasu na daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments