Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Muhimman Wurare A Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hezbollah ta tarwatsa wasu muhimman kayan ayyukan leken asiri na haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hezbollah ta tarwatsa wasu muhimman kayan ayyukan leken asiri na haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare-hare kan kayayyakin ayyukan leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wuraren Al-Jarda da Al-Raheb, inda suka yi musu luguden wuta kai tsaye, lamarin da ya kai ga tarwatsa su. An kuma yi ta jin karar sautin gargardi na neman gudun yahudawa zuwa maboyansu na karkashin kasa a yankuna da dama na arewacin yankunan da aka mamaye, ciki har da Kiryat Shumona.

Kungiyar ta Hizbullah ta kaddamar da hare-haren ne a matsayin mayar da martani kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamaya suka kai kan kauyukan kudancin Lebanon da jaddada goyon bayan ga Gaza da kuma ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare-haren ne kan wani ginin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suke amfani da shi a matsugunin Al-Manara kuma hare-haren sun samu cibiyar kai tsaye, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara a cikinsa da kuma tabbacin halakar wasu sojojin mamaya.

Haka nan rundunar sojin mamaya ta amince da tashin gobara a yankin Al-Manara da dajin Ramim da ke yankin Upper Galilee sakamakon fashewar wani jirgin yaki maras matuki ciki na kungiyar Hizbullah, kamar yadda Majalisar yankin Marom Galilee ta amince da cewa wata gobara ta tashi a yankin Avivim sakamakon faduwar makamai masu linzami biyu na kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments