Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji  A Yankin Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da matakin da isra’ila ke dauka na tsauraran mataken shigar da kayan agaji zuwa yankin

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da matakin da isra’ila ke dauka na tsauraran mataken shigar da kayan agaji zuwa yankin gaza musamman bangaren sansanin yan gudunn hijira da kuma tanti-tanti  da aka yi.

Kakakin kungiyar hamas Hazem Qaseem ya jaddada cewa mafakar da suka rage a yankin tantuna ne da aka yi marasa karko, da ba za su iya jurewa iska ko yanayin sanyi ba.

Yace har yanzu isra’ila tana bari a shiga da wani adadi kadan ne zuwa yankin gasa na kayayyakin agaji, wanda  ba zai wadatar da abubuwan bukatatun yau da kullum na rayuwa ba ga yawan alummar dake bukatar agaji a daidai lokacin da ake fuskantar mawuyacin yanayi dake bukatar taimakon gaggawa,

Qassem ya yi  kira ga masu shiga tsakanin da sauran kasashen duniya da su dauki mataken gaggawa kan isra’ila domin  ta bada damar shigar da kayayyakin agaji ga tantuna da aka yi kafin yanayin sanyi ya kara yin tsanani a yankin gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments