Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana rashin amincewarta da kakkausar suka ga rahoton da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya fitar kan cin zarafin mata da ke da alaka da rikice-rikicen makamai, wanda ya hada da kungiyar ta Hamas a cikin jerin bakin littafin wato “blacklist”, yayin da Guterres ya yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yari.
Kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Juma’a cewa: Wannan matakin bai dace ba a bisa doka, ta kuma yi gargadin cewa; “wannan karan-tsaye mai tsauri na nuni da karkacewa mai hatsarin gaske daga ka’idar daidaito a gaban dokokin kasa da kasa da kuma nuna kyama ga manufofin Majalisar Dinkin Duniya, da yin barazana ga amincinsu tare da mayar da su wani makami na wanke laifuffukan ‘yan mamaya.”
Kungiyar ta jaddada cewa: Wannan shawarar ba ta dogara a kan bincike mai zaman kansa da nisantar nuna son kai ba, sai dai ta dogara ne kawai kan labaran siyasa da kage na ‘yan mamayar Isra’ila gaba daya, ba tare da gudanar da wani bincike na rashin son zuciya ba, ko kuma yin magana da wadanda ake zargin.