Kungiyar Hamas Ta Jaddada Rashin Yiwuwar Korar Falasdinawa Daga Yankin Zirin Gaza

Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile

Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza

Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara.

Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar hare-haren bama-bamai da wuce gona da iri, kuma za su ci gaba da tsayin daka kan kasarsu tare da dakile duk wani shiri na neman tilasta musu gudun hijira daga muhallinsu zuwa wasu kasashen makwabta.

Hamas ta jaddada cewa: shirin korar al’ummar Palasdinu daga Gaza ba zai yi nasara ba, kuma zai fuskanci kalubalen Falasdinawa, Larabawa da kuma al’ummar musulmi wadanda suka yi watsi da duk wani shiri na raba Falasdinawa da muhallinsu zuwa gudun hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments