Kungiyar Hamas Ta Ce HKI Ta Kasa Samun Nasara Kan Kungiyar A Gaza

Usama bin Hamdan wakilin kungiyar Hamas a kasar Lebanon ya bayyana cewa, sojojin HKI sun kasa samun nasara a kan kungiyar Hamas a Gaza da

Usama bin Hamdan wakilin kungiyar Hamas a kasar Lebanon ya bayyana cewa, sojojin HKI sun kasa samun nasara a kan kungiyar Hamas a Gaza da kuma samun galaba a kan yankin  a fafatawa da ita da suka yi na fiye da shekara guda.

Tashar talabijin ta Aljazeerah da ke birnin Doha na kasar Qatar ta nakalto Hamdan yana fadar haka a hira ta musamman da tashar a jiya Asabar.

Ya kuma kara da cewa sojojin HKI da suka shiga Gaza ba sa neman mayakan Hamas ko jihadul Islami ko kuma mayaka na sauran kungiyoyin Falasdinawa a Gaza, maimakon haka sun koma kan mata da yara wadanda basa dauke da makami suna kashesu.  

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin HKI suka fara kaiwa Falasdinawa a Gaza hare hare da nufin kwato yahudawan da kungiyar da wasu kungiyoyin Falasdinwa suke tsare da su a Gazar. Har’ila yau da nufin shafe kungiyar Hamas da kuma kwace iko da zirin gaza daga hannunta. Amma a halin yanzu fiye da shekara guda kenan sun kasa samun ko da guda daga cikin manufofinsu a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments