Kakakin rundunar shahidan Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Abu Ubaida, ya sanar da cewa: A kwanakin baya-bayan nan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai harin bam a wani wurin da akwai wasu fursunonin yahudawan sahayoniyya, ya kara da cewa; Sojojin mamayar sun sake kai harin bam wurin domin tabbatar da cewa sun kashe fursunonin yahudawan.
Abu Ubaida ya yi kuma nuni da cewa: Akwai bayanan sirri da ke fayyace cewa makiya da gangan suka kai hare-haren bama-bamai a duk wurin da suke tsammanin ana tsare da fursunonin yahudawan sahayoniyya da nufin kashe su da masu gadinsu.”
Ya kuma jaddada kokarin da ‘yan gwagwarmaya suka yi na kubutar da fursunonin yahudawan, kuma sun yi nasarar zakulo daya daga cikinsu daga karkashin baraguzan gini, kuma ba a san makomarsa ba a halin yanzu.
Abu Ubaida ya dora alhakin kisan gilla kan fursunonin yahudawan a kan mai aikata laifin yaki Netanyahu da gwamnatinsa da kuma sojojin ‘yan sahayoniyya cikakken alhakin, da kuma rayuwar fursunonin su.
Wannan hare-haren suna zuwa ne bayan ci gaba da tattaunawa kan hanyar gudanar da yarjejeniyar musayar fursunonin, tun farkon wannan wata na Disamba, kuma ana kusan cimma yarjejeniyar musayar fursunonni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinu da gwamnatin yahudawan mamaya.