Kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa asibitin Kamal Adwan a Gaza.
“Kungiyar ta jaddada cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa fannin kiwon lafiya, ciki har da kai hari, da farmaki a asibitoci da kama ma’aikatan kiwon lafiya, ya zama babban cin zarafi ga tanadin dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma shawarwarin Majalisar Dinkin Duniya da suka dace,” inji OIC.
Kungiyar ta kuma yi kira da “dakatar da wannan mummunar ta’addancin sojojin Isra’ila”, da kuma mutunta ma’aikatan kiwon lafiya, marasa lafiya da wadanda suka jikkata.
Gwamnatocin kasashen Saudiyya da Jordan da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa duk sun fitar da irin wannan sanarwa inda suka nuna bacin ransu game da harin na kan asibitin Kamal Adwan.
Dama tun farko hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce Isra’ila ta ruguza tsarin kiwon lafiya a Gaza, tana mai bayyana harin na Kamal Adwan da babban abun damuwa.
Sanarwar ta ce “Wannan farmakin da aka kai a asibitin Kamal Adwan ya zo ne bayan tsaurara matakan hana shiga ga hukumar ta WHO da abokan huldanta Zirin, da kuma kai hare-hare a kusa da cibiyar tun farkon watan Oktoba,” in ji sanarwar.
“Dole ne a kawo karshen wannan, kuma dole ne a kare marasa lafiya da kuma tsagaita wuta!” inji WHO.
WHO, ta ce ayyuka sun tsaka cik a babban asibitin na kamal Adwan na karshe dake aiki a Gaza bayan farmakin ISra’ila.