Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Ce: Sanarwar Trump Kan Batun Yemen Gazawa Ce Ga Netanyahu

Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar

Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu

Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari da cewa “Sanarwar Trump wata nasara ce da ta raba goyon bayan da Amurka ke baiwa gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yar mamaya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments