Kungiyar Abokan Yarjejeniyar M.D.D Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ke Kai Wa Kan Iran

Kungiyar ‘Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya’ ta yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan Iran Kasashe mambobin kungiyar aminan yarjejeniyoyin

Kungiyar ‘Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya’ ta yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan Iran

Kasashe mambobin kungiyar aminan yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da wata sanarwa ta musamman inda suka yi kakkausar suka kan wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Sanarwar ta yi la’akari da harin hadin gwiwa ta sama da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar a ranar 13 ga watan Yuni a kan wasu wurare da dama a Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkata wasu daruruwa da suka hada da mata da kananan yara da masana kimiyya, matakin da ya saba wa Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa.

‘Yan kungiyar sun kuma yi Allah wadai da harin ganganci kan fararen hula, da wuraren zaman jama’a, da kuma cibiyoyin nukiliyar na zaman lafiya, suna masu gargadin cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da watsuwar kayan aikin kimiyya da zai zama babbar barazana ga rayuwar fararen hula da muhalli.

Kungiyar ta yi kira da a tsaya tsayin daka kan amfani da karfi a kan Iran, tana mai jaddada nauyin da ke wuyan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na kiyaye manufofi da ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar.

Har ila yau, ta jaddada aikin babban daraktan hukumar ta IAEA na yin Allah wadai da hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kaiwa kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments