Wata kotu a kasar Sweden ta yanke hukuncin daure Rasmus Paludan wani dan siyasa dan asalin kasar Sweden wanda ya ci zarafin kur’ani mai tsarki sau da dama tare da cinna masa wuta.
A cewar shafin yanar gizo na Elkomps, kotun Malmö da ke Sweden ta yanke wa dan siyasar Rasmus Paludan hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bayan ta same shi da laifin yada kiyayya da wariya.
Kotun ta samu Paludan ne da laifi bayan da ya yi kalaman batanci ga musulmi, Larabawa da kuma ‘yan Afirka a cikin shirinsa na kona kur’ani a Malmö a shekara ta 2022.
A cewar masu gabatar da kara, Paludan ya yi kalaman wariya a kan Musulmi, Larabawa da kuma ’yan Afirka a taruka biyu a Malmö a watan Afrilu da Satumba 2022.
Dangane da haka ne ofishin mai gabatar da kara ya sanar da cewa Palodan ya wulakanta kur’ani mai tsarki tare da cinna masa wuta a daya daga cikin wadannan tarukan guda biyu.
Baya ga yada kiyayyar kabilanci, kotun ta samu Paludan da laifin zagin wani mutum mai suna Long Conte, da kuma umarce shi da ya biya diyyar kudi euro 40,000 ga wannan mutum.
Conte, wanda ke zaune a Malmö, ya ba da shaida a kan Paludan, yana mai cewa dan siyasar mai matsanancin ra’ayi ya maimaita kalmar “koma Afirka” sau 35 a gabansa kuma ya ce ‘yan Afirka ba sa da wurin zama a kasar Sweden.
A cikin wata sanarwa da shugaban kotun da ta yi shari’ar Paludan Nicholas Souderberry ya fitar ya ce: “An halatta maganganu masu mahimmanci game da Musulunci, amma dole ne su kasance cikin mahallin tattaunawa da mahawara.” A cikin waɗannan lamuran da suka shafi Paludan, babu irin wannan tattaunawa ko muhawara, maimakon haka ma maganganunsa sun kasance na cin mutunci da cin zarafi ga musulmi.
Paludan yana da shedar zama dan kasar Sweden da Denmark, kuma ya shahara a kasar Sweden saboda shirya tarurruka na kona kur’ani a gaban zaben ‘yan majalisar dokoki na 2022.