226-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Al-Kur’ani mai girmako cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare damu a cikin shirimmu na yau.
///… Madalla, masu sauraro, idan kuna tare da mu, a cikin shirimmu na ya gabata a kuma sirar Imam Al-Hassan dan Ali (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, mun tsaya inda muke ci gaba da kawo maku mabiya Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (a) wadanda Mu’awiya dan Abusufyan da ma’aikatansa suka kashe ko suka cutar da su.
A cikin shirimmu da ya gabata mun karasa magana dangane da Amru dan Al-Hamkul Khuzaa’i, Juwairiyya dan Mashar Al-Abdi, Awfi dan Hisen, Abdurrahman Al-hadrami. Mun bayyana yanda ya bada Umurni aka rusa gidajensu, sannan ya sake bada umurni aka daina karban shaidarsu.
Sannan mun bayyan manufar daukar dukkan wadannan matakan a kan mabiya Amirul muminina (a), wanda kuma shi ne batar da su da kuma shafe sunan Amirulmuminina (a) daga doron kasa. Ko kuma shafi musulunci na asali wanda All..T ya saukarwa manzon All..(s). Amma All..ya yi alkawalin kammala haskensa ko da kafirai basa so.
Ya kashe wasu ya bada umurni a rusa gidajen wasu, ya hana a karbi shaidarsu, ya watsa tsoro cikin zukatansu, ya sa aka jefa wasu a gidajen yari har sukamutu ya sa wasu sun tsorata sun guda daga kasashen larabawa suka shiga wajen ajamawa suka boye kawukansu, don tsira daga musiba daga bala’in mu’awiya da ma’aikatansa. Wasu kuma ya sa ma’aikatansa suka kamasu suka zo da su wajensa inda ya kaskantasu.
Daga cikin wadanda ya jefa a gidan yari har suka mutu akwai.
01-Muhammad Ibnu AbuKhuzaifa: Muhammad dan Abu-Khuzaifa, yana daga cikin salihan bayi , wadanda mutane da dama suka sanshi da aikata alkhairi, yana daga cikin masu umurni da ayyukan Alkhairi, da kuma hani daga mummunan ayyuka.
Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) ya fada dabgabe da shi da wasu masu kama da shi. {lalle masu suna Muhammadu sun dage sai an bar sabon All..} sannan ya ambaci sunayensu guda guda ya zo kan sunan Muhammad dan Abu Khuzaifa.
Dan Abukhuzaifa ya luzmci Aliyu dan Abitalib (a), amma da aka kashe shi(a), sannan Mu’awiya ya sami iko a kan musulmi, sai mu’awiya ya sa aka kama shi, aka kawo gabansa, sannan ya so ya kashe shi sannan ya fasa, sai ya ce a jefa shi a gidan kaso, ya dade har kusan aka manta da shi.
Sai wata rana Mu’awiya ya tuna da shi sai ya ce: Shin ba zaku kawo wannan wawan ba, Muhammad dan Abu-Khuzaifa, mu aibata shi, mu fada masa batar da yake kai, mu umurceshi ya zagi Aliyu (a). ? sai suka ce babu laifi, sai aka fito da shidaga gidan yari aka kawo shi gaban Mu’awiya.
Sai yace masa: Ya Muhammad shin lokaci bai yi ba da ka gane gaskiya, ka bar batan da kake kai, na goyon bayan Aliyu dan Abitalib(a)? Baka fahinci cewa an kashe Uthman a matsayin wanda aka zalunta ba? Sannan cewa Aisha, da Talha da Zubair sun fito ne, suka yaki Aliyu (a) saboda neman jininsa? Baka fahinci cewa Aliyu (a) ne ya sa aka kashe shi ba? Kuma ga shi mu a nan muna neman fansar jininsa ne?.
Sai Muhammad Ya ce: Ka san cewa ni nafi kowa saninka saboda dangantaka, sannan na fisu sanin halayenka. Sai mu’awiya yace: Gaskiya ne. Sai muhammad ya ce: (Na rantse da All.. wanda babu abin bauta da gaskiya sai shi, ban san wani wanda ya fi kowa hannu a wajen zubar da jinin Uthmanu ba, ya kuma ingiza mutane saboda haka kamarka. A lokacinda shi Uthman ya sanyaka gwamnan Sham. Da kuma wadanda suka kasance kamarka. An yi lokacinda Muhajiruna da Ansar suka bukaci Uthman ya sauke ka daga kujerarka, amma ya ki. Har saida suka yi abinda suka yi da shi kamar yanda ka sani, kuma na rantse da All..ba wadanda suke da hannu wajen kashe Uthmanu daga farko har karshe kamar Zubair da Talha da kuma Aisha. Su ne suka bada shaidar cewa ya aikata laifi, suka ingiza mutane a kansa, Abdurrahman dan Auf ya shiga cikinsu, da dan Mas’udu, da Ammar da dukkan Ansar). Sai Mu’awiya ya ji tsoron abinda yake fada, sai yace: Haka ya faru?. Na rantse da All…, na kuma shaida! baka guce ba, kana nan kamar yanda na sansa kafin musulunci da bayan musulunci kan hali guda. Musulunci bai kareka da koma ba, bai kuma rage ka ba. Kuma alamar haka yana nan a fili a wajenka.
Sai Muhammad yace: Kana aibatani da son Aliyu?, alhali, dukkan Muhajirun da Ansar, masu yawan azumi masu yawan sallah sun fito yaki (Jamal Da Siffin) tare da shi, kai kuma, wadanda suke tare da kai yayan munafukai ne, da yentattun bayin manzon All..(s) bayan fatahin Makka wato Tulaka,… ka yaudaresu da addininsu kamar yanda suka yaudaru da duniyarka. Na rantse da All.. Ya mu’awiya, abinda ka aikata ba bisa rashin sani bane, haka su ma abinda suka yi ba bisa jahilci bane, a lokacinda suka amince da fushin All..a kansu tare da biyayya a gareka.
Na rantse da All…ban gushe ba ina son Aliyu. (a). don All..da kuma manzonsa (s). kuma zan ci gaba da kinka saboda All..da manzonsa (s) matukar rayuwa ta.
Sai Mu’awiya: Lalle ina ganin baka gushe ba kana kan batarka, ko maida shi gidan yari yari. Sai suka maida shi gidan yari, bai dade ba ya mutu a cikinsa.
02-Abdullahi dan Hashim Al-mirkal. Daya daga cikin masoyan amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), wanda shi ma Mu;awiya dan Abusufyan ya wahalar da shi ya kuma tsoratar dashi, shi ne Abdullahi dan Hashimul Mirkal.
Mu’awiya dan Abusufyan yana matukar kiyayya da shi, saboda sonsa ga Amirulmuminina (s) da kuma abinda mahaifinsa Hashimul Mirkal yayi da mutanen sham a yakin siffin. Iran yakin da mahaifinsa yayi da mutanen sham a Siffin ya sa Mu’awiya ya fara tunanin gudu daga yakin. In ba don yaudarar da suka yiwa wasu daga cikin sojojin Imam Ali (a) ba.
Mu’awiya ya rubutawa ma’aikacinsa a Kufa da umurnin ya kama shi. Kuma ga wasikar da ya rubuta masa dangane da haka.
“…bayan haka, idan wasika ta ta isa gareka, kan je unguwar banu Makhzum ka gudanar da bincike gida gida, sai ka isa gidan wata yar kabilar Makhzumi mai suna kaza, ka fitar da Abdullahi dan Hashimul Mirkal, ka aske kansa, ka ka sanya masa rigar gashin dabbobi, ka daure hannayensa, ka daure hannayensa kan wuyarsa, ka dorashi kan rakumin, babu sirdi babu ko wani shimfida ka aiko da shi zuwa wajena”.
Ziyad ya je unguwar Makhzumin a Kufa ya bi gida gida saida ya fito da Abdullahi dan Hashim, ya kuma aika shi zuwa sham da kamannin da Mu’awiya yake so. Dan Hashim ya isa sham a ranar Jumma’a a ranar da Mu’awiya yake ganawa da manya manyan Kuraishawa sai ya ga dan Hashim ya karaso. Sai ya juya wajen Amru dan Asi yana cewa, Ya amuru ka gane wannan matashin? Sai yace bai gane shi ba, sai ya ce: shi ne wanda babbansa yace kaza da kaza a shiffin sai ya rera wata kasida wacce Hashimul Mirkal ya rerta a yakin Siffin .
Sai Amru dan Asi ya ci gaba da aibata shi da kuma mahaifinsa. Sannan shi ma Abdullahi ya mayar masa da martani. Ya kuma yi ta jayayya da Amru da kuma Mu’awiya a cikin kasidu . Amru dan Asi ya bukaci Mu’awiya ya kashe shi, sannan dan Hashimu saboda abinda mahaifa Hashimul Mirkal ya yi da mutanen sham a siffin. Hashimul Mirkal dai yana daga cikin kwamandoji Amirul mumina Aliyu dan Abitalib (a) a yakin Siffin. Ya kuma jagoranci sojojin suk murkushe sojojin Mu’awiya har sai ya kai ga mu’awiya ya tabbatar da cewa Aliyu (a) ya sami nasara a kansa, ya kuma fara tunanin gudu daga yakin. Sai Amru dan Asi ya kawo shawarar daga mushafi, wanda kuma ya sami nasarar rikita sojojin Imam Ali(a) yasa da dam daga cikinsu suka daina yi masa biyayya. Ta nan ne mu’awiya ya kubuta aka kawo karshen yakin.
Amma shi Hashimul Mirkal, an yake kafarsa a yakin sannan ya yi ta zubar da jini har yayi shahada a siffin. Daga karshe dai Mu’awiya ya bada umurni a jefa shi cikin a gidan yarinsa. Bayan ya tsoratar da shi.
03- Abdullhi dan Khalifatu Attaee. Dan Khalifatu Attaee, ya shahara da son Amirulmumina Aliyu dan Abitalib (a) a cikin musulmi, kuma sun hadu da shi a lokacinda yak ama hanyarsa (s) zuwa Basra, sai ya ce masa, godiya ta tabbata ga All..wanda ya mayar da gaskiya zuwa ga ma’abucinsa. Ya sanya shi a inda ya dace. Ko da kuwa wasu mutane basaso. Hakika wallahi sun ki Mohammadu (s) sun yi jayayya da shi sun kuma yake shi, All..ya mayar masu kaidinsu a kansu. Ya mayar masu da sharrinsu. Na rantse da All..zan yi yaki tare da kai a ko ina don kare hakkin Manzon All..(s).
Wannan maganar tasa ta nuna basirarsa, da sanin hakkin Imam Ali(a) don haka ya kasance cikin wadanda suka luzumceshi, ha rya zama cikin wadanda Amirul muminina (a) yake shawartarsu a cikin manya manyan al-amura.
A lokacinda Mu’awiya ya kashe Hijri dan Adiy Al-Kinda, Abdullahi dan Khalifatah Attaee yana daga cikin wadanda suka yi inkarin siyasar banu umayya na kisar bayin All..masoya Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Yana daga cikin wadanda suka goyi bayan Hijru a lokacinda ya jagorancin tawaye a kufa. Ubaidullahi dan Ziyad ya umurci jami’an tsaronsa su kama masa Abdullahi dan Khalifah Attaee, suka je suka yi ta bincike a cikin kufa har sai da suka gano shi suka kama shi, bayan fafatawa mai yawa da shi da wadanda suke kare shi.
Amma Yaruwansa wacce ake kira ‘Annawwar, ta taimaka masa, ta je wajen danginsu Attaeeyun a kufa ta ce masa, yak u dangin Taaiyyun ba zaku yi amfani da takubbanku da kuma harsunanku don kubutar da Abdullahi dan Khalifa ba. Sai suka amsa kiranta suka farwa yansandan dan Ziyad suka dakesu har suka gaji suka bar Abdullah dan Khalifa Attaaee.
A lokacinda yansandan dan Sumayya suka koma wajensa suka kuma fada masa abinda ya faru, sai ya sa aka kira masa shugaban kabilar Taai gaba daya, sahabin Manzon All..(s) wanda ake kira Adi Dan Khatam Attaaee. A lokacinda Adi ya zo, sai yace masa ya je ya kawo masa Abdullahi dan Khalifa. Sai Adi yace masa ba zai kawo shi ba har’abada. Kana son in kawo maka dan ammina ka kashe shi. Wannan ba zai yu ba har’abada. Na rantse da All..da yana karkashin kafata a na a inda nake tsaye, da ban dagata ba don ka kama shi ba.
Daga nan sai Ziyad yayi Fushi, kuma ya ji tsaro, sai ya umurci yansandansa su jefa Adiy dan Khatam Attaee cikin gidan Yarinsa. Amma ba’a dade ba, sai dukkan mutanen Yemen a kufa da. Ko kuma yan dangin Rabii saida suka zo wajen Ziyad suna masa Magana a kan tsare Adiya dan Khatam da yayi. Sun yi masa Magana kan matsayinsa, da kuma yawan mabiyan da yake da su a Kufa, idan ya bari abun ya kara lalacewa, suna iya hanashi Mulki, saboda yanda suke girmama shi.
Daga karshe, Ziyad ya fahinci abinda suke nufi. Sai ya sa ake sakeshi tare da sharadin kada ya sake ganin Abdullahi dan Khalifa Al-kindi a Kufa, wanda Adiy ya amince.
Don haka Abdullahi, tare da taimakon yar’uwansa da kuma shugaban kabilar Taai a Kufa ya kubuta daga kisa a hannun Ziyad dan Sumayya, ya kuma bar Kufa ya koma Jabalain.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu
================================================.